FATAWAR RABON GADO (57)|Dr jamilu yusuf zarewa

FATAWAR RABON GADO (57)
Tambaya?
Assalamu alaikum Mlm ina da tambaya, idan mace ta mutu ta bar 'ya mace guda daya, da dan"uwa shaqiqi daya, da jikokinta na da namiji 24 maza 14 mata, dan Allah mlm yaya rabon gadon zai kasance?, Allah ya saka da"alkhairi.
Amsa:
Wa alaikum assalam, Za'a raba abin da ta bari gida biyu, a bawa 'Yarta kashi daya, ragowar sai a bawa jikokinta, duk namiji ya dau Rabon mata biyu.                          
Allah ne mafi sani.
Amsawa: Dr Jamilu Zarewa                                   24/9/2016

Share this


0 comments:

Post a Comment