A KAN KISHIN KASAR NIGERIA BUHARI ZAI IYA RABUWA DA KOWA

A KAN KISHIN KASAR NIGERIA BUHARI ZAI IYA RABUWA DA KOWA
Daga Bappah Abubakar
Hajiya Safinatu Yusuf Mani matar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta farko Allah Ya jikanta da Rahama Allah Yasa ta huta.
Hajiya Safinatu Muhammad Buhari Allah Ya mata baiwar ilmi kamar yanda wani marubuci Mr Abiyamo ya wallafa akan tarihin rayuwarta, domin takan iya karantawa tare da rubutawa da harshen larabci, ta kuma halarci makarantar horar da malaman makaranta dake garin Katsina inda ta samo takardan shedan Grade II a shekarar 1971.
Marigayiya Safinatu ta fara haduwa da shugaban kasa Muhammadu Buhari ne a shekarar 1966 lokacin tana da shekaru 14, shikuma Buhari a lokacin yana matsayin matashin manjo a gidan soja, sai shi Buhari da abokinsa marigayi Major Gen. Shehu Musa 'Yar Aduwa suka tafi Lagos domin sugana da mahaifin Safinatu wato Alhaji Yusuf Mani wanda a lokacin yana matsayin sakataren ministan birnin tarayya na Lagos Alhaji Musa 'Yar Adua, a lokacin ne shugaban kasa Buhari ya fara ganin Safinatu a gidan mahaifinta.
Tundaga wannan ziyara ta farko, sai Buhari ya dinga zuwa Lagos akai-akai domin ziyartan masoyiyarshi marigayiya Safinatu, har suka shaku da juna suka amince a matsayin masoyan juna.
Shugaban kasa Buhari yana cikin soyayya da matarshi Safinatu sai yakin basasan Nigeria ya barke aka turashi fagen yaki a shekarar 1967.
A lokacin sai masoyiyarshi Safinatu ta shiga cikin wani yanayi na damuwa kamar yanda ta bayyana da bakinta, tace; haka tacigaba da yimasa addu'ah kullun ba gajiyawa har aka kammala yakin basasa.
Lokacin da shugaban kasa Buhari yana a fagen yakin basasa, kullun damuwarsa shine kasarsa Nigeria da kuma tunanin masoyiyarshi Safinatu, Allah Yasa aka kammala Yakin a shekarar 1971 sukayi aure tana da shekaru 18.
Safinatu matar shugaban kasa Buhari matace mai mutunci da ilmi wanda ya hada na addini da na boko, soyayyar da take nunama shugaban kasa Buhari bayyananne ne a wajen wadanda suka sansu tare.
Lokacin da sojoji sukayi juyin mulki wa gwamnatin shagari bayan da abubuwa suka tabarbare a cikin kasa, cin hanci da rashawa yayi kakatutu, sai sojojin suka duba nagartaccen soja Muhammadu Buhari mai kishin kasa wanda ya kyamaci ayyukan cin hanci da rashawa suka bashi ragamar mulkin kasa, wanda hakan yana nufin Buhari bashine yayi juyin mulki ba.
Buhari da yazo sai ya toshe hanyar cin hanci da rashawa, wadanda suka zaboshi sunyi tsammanin zai bude musu kofa suyi ta satar dukiyar kasa, amma sai Buhari yasa akayi ta kama barayi ana kullewa a gidan yari, ya kuma gabatar da shirinsa na yaki da rashin da'a a cikin kasa, a kokarinsa da yakeyi a wancan lokaci wajen inganta tattalin arzikin kasa da yaki da cin hanci da rashawa, sai yakasance talakawa sun fada cikin yanayi na yunwa da wahalar rayuwa, abubuwa suka kuntatawa 'yan Nigeria, sai aka samu wasu sojoji handamammu karkashin jagorancin Gen. Babangida sukaje suka kifar da gwamnatin Buhari, suka kamashi suka jefa a gidan yari.
Sai ya kasance a lokacin da Buhari yake gidan yari yayi nesa da iyalanshi wato marigayiya Safinatu da 'ya'yansu da suka haifa, babu mai daukar nauyinsu, to sai Gen. Babangida ya dinga aika mata da wasu kudade da zata sarrafa ita kuma tana karba, wannan shine abinda yaja Buhari yana fitowa daga gidan yari ya saki matarshi kuma masoyiyarshi Safinatu a dalilin wannan kudade da take karba daga wajen Gen. Babangida.
Haka Gen. Babangida ya kare mulkinsa aka hambarar dashi batare da ya tabuka komai ba a cikin kasarmu Nigeria, sai abubuwa ma sukacigaba da dagulewa, wanda inda ace sun kyale Buhari da Nigeria ta gyaru tundaga wancan lokaci.
To don Allah jama'a idan har shugaban kasa Buhari zai iyasa sakin matarshi don ta karbi tallafi daga wajen mabarnata kasarmu Nigeria, shin kuna ganin bazai iya sake wannan mata Aisha da yake tare da ita ba matukar tayi abinda ya wuce gona da iri?, domin yadai tabbata akan kishin kasar Nigeria Buhari zai iya rabuwa da kowa har matarshi, don yayi an shaida.
Wata shakikiyar Buhari tace ko itane tayi sata akan idon Buhari ta tabbata sai yasa an kamata an kulle.
Furucin da Aisha Buhari tayi matukar dai ba da sanin shugaban kasa Buhari tayi ba, to fa akwai matsala da zai iya faruwa nan gaba, amma muna fatan Allah Ya kiyaye.
A yau dinnan sai da Dr. Idris Ahmed ya fitar mana da takaitaccen tarihin Aisha Buhari, Buhari ya aureta a lokacin karatun sakandare ne kadai gareta, amma haka yacigaba da tallafa mata har takai yau tana da shaidan karatu a matsayin digiri na biyu, banda tallafa mata da tayi wajen gudanar da harkokin kasuwanci, wanda zamu iya cewa ta tara dukiyan da shi Buhari bai mallaka ba.
Don Allah mu sake jaddada wannan maganar cikin zukatanmu shine; indai ba wani sako akeso a isarwa 'yan Nigeria ba, kuma duk furucin da Aisha tayi akan mijinta indai ba da saninshi bane, to fa akwai babban matsala.........jamuje baba buhari ya Allah dai yaja da nisan kwana mai amfani

Share this


0 comments:

Post a Comment