FATAWAR RABON GADO (64)|DR JAMILU YUSUF ZAREWA

FATWAR RABON GADO (64)
Tambaya?
Assalam alaikum,
MACE TA MUTU TA BAR: 1.MIJI 2.MAHAIFIYA 3.'YAR UWA SHAKIKIYA 4.'YAN UWA MAZA DA MATA UWA DAYA 5.'YAN UWA UBA DAYA MAZA DA MATA ALLAH YASAKA DA ALKHAIRI MALAM
Amsa:
Wa alaikum assalam, Za'a raba abin da ta bari gida: 9, (Auli daga shida) a bawa miji kashi: 3, sai a bawa uwa kashi: 1, 'yar'uwa shakikiya za ta dauki kashi:3, sai a bawa 'yan'uwan da aka hada uwa daya kashi biyun.
Allah ne mafi Sani.
8/10/2016
Amsawa: Dr Jamilu zarewa.

Share this


0 comments:

Post a Comment