FATAWAR RABON GADO (66)|DR JAMILU YUSUF ZAREWA

FATAWAR RABON GADO (66)
Tambaya?
Assalamu alaikum
Da fatan Malam yana cikin koshin lafiya. Don Allah a taimakeni da wannan: mata ta rasu babu miji, uwa ko uba, saidai diya mace da 'yan uwa mata guda biyu shakikai. Yaya rabon gadon zai kasance? Ka huta lafiya, na gode.
Amsa :
Wa alaikumus salam,
Za'a raba abin da ta bari gida biyu, a bawa' Yarta kashi daya, sai a dauki ragowar a bawa 'yan'uwan ta.
Allah ne mafi sani                      16/10/2016
DR JAMILU ZAREWA

Share this


0 comments:

Post a Comment