SHIN SUNAN RUMAISA'U YANA SA ASALI ?|DR JAMILU YUSUF ZAREWA

SHIN SUNAN RUMAISA'U YANA DA ASALI?
Tambaya?
Assalamu alaykum
Malam menene asalin sunan rumaisa ko rumassa'u kuma a zamanin Annabi akwai maisunan in akwai a bani tarihin ta?
Amsa:
Wa alaikum assalam, Rumaisa'u suna ne na daya daga cikin sahabbai mata, ita ce ta haifi Anas Dan Malik hadimin Annabi S.a.w, ita ce ta kai shi wajan manzon Allah don ya dinga masa hidima, ta auri Abu-dalha, sahararren sahabi mutumin Madina,  an fi saninta da sunan Ummu-sulaim. Tana daga cikin mataye masu hikima, akwai mahaddatan Alqu'ani da yawa da suka fito daga tsatsonta.
Allah ne mafi sani
11/10/2016
Dr Jamilu Zarewa

Share this


0 comments:

Post a Comment