Ambaton Allah shi ne rayuwar Zukata Dr Muhammad sani umar R/lemo

Ramadaaniyyat 8 (1438H)
Ambaton Allah shi ne rayuwar Zukata

Allah (S.W.T) ya umarci Annabi Zakariyya (A.S) da ya  ambaci Allah diyawa. Wannan yana nuna maka falalar ambaton Allah. Allah ya togace ambatonsa daga cikin abin da Zakariyya ba zai iya furta wa ba da bakinsa. Domin Ambaton Allah (S.W.T) shi ne abincin gina zukata, idan babu shi, zuciya za ta mutu ne murus. Don haka mutum yana iya hakura ya bar magana, amma ba zai iya hakura ya bar ambaton Allah ba. Ibn Jarir ya ruwaito a cikin Tafsirinsa daga Muhammad bn Ka’ab ya ce: “Da a ce Allah zai yi wa wani sauki ya bar ambatonsa to da ya yi wa Annabi Zakariyya in da ya ce: (Alamarka ita ce ba za ka iya magana da mutane ba tsawon kwanaki uku sa dai ishara, kuma ka ambaci Ubangijinka diyawa). [Dubi, At-Tabri, At-Tafsir, Juzu’i na 5, shafi na 391].

Share this


0 comments:

Post a Comment