Fatawar Rabon Gado (132) Dr Jamilu Yusuf Zarewa


Tambaya

Assalamu alaikum dr. Ina maka fatan alheri da fatan anyi sallah lfy don Allah dr. ina da tambaya kamar haka? Mutum ne ya mutu ya bar mace da yara, maza 9 da mata 12 da kudi naira miliyan daya da dubu dari, to malam ya kason zai kasance Allah ya kara lfy.

Amsa

Wa alaikum assalam, Za'a raba kudin gida takwas, sai a bawa matar mamacin (137,500), ragowar (962,500) sai a kasa su gida talatin, kowanne namiji ya dau kashi biyu, tun da su tara ne, kowacce mace ta dau kashi daya tun su (12).
Allah ne mafi sani

Amsawa

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
06/09/2017

Share this


0 comments:

Post a Comment