Hudubar Jumu'ah Daga Haramin Makkah Mai Albarka: Maudhu'i: Mika Wuya ga Allah Dr Mansur SokotoLiman: Sheikh Khalid Al-Ghamidi

Mai Fassara: Dr. Mansur Sokoto

Rana: 17/12/1438H

Maudhu'i: Mika Wuya ga Allah


Liman ya yi doguwar gabatarwa mai cike da hikima dauke da godiyar Allah a kan shar'anta aikin Hajji da ya yi don amfani iri iri da musulmi suke samu a ciki.

Limamin ya kira Alhazai su gode ma da ya zabo su daga cikin al'ummar musulmin duniya don su yi wannan ibada mai girma

Ya zayyano darussa muhimmai da ya kamata Alhaji ya tafi da su gida bayan kammala wannan aiki.

Daga cikin wadannan darussa liman ya yi dogon sharhi a kan maganar Tauhidi da mika wuya ga Allah da Manzonsa. Ya ce duk ayyukan Hajji da'a ne da biyayya ga umurnin Allah da aikin Manzonsa.

Limamin ya bayyana darajojin Annabi Ibrahim (AS) wanda duk sawunsa ne ake bi ga aikin Hajji. Ya ce Annabi Ibrahim shi ne wanda ya kai matuka wajen bin umurnin Allah shi da iyalansa; matarsa Hajar da dansa Ibrahim. Yau ga shi duk ayyukansu ne muke kwaikwaya a cikin aikin Hajji shekara bayan shekara.

Wajibi ne mu koma ga Allah muna masu amfani da wadannan darussa da muka koya a cikin wannan ibada mai girma.

A cikin huduba ta biyu ma limamin kara fadada magana ya yi game da zancen mika wuya ga Allah da kakkabe aikin shaidan da shubuha da son zuciya. Idan kana mumini ba ya dacewa ka gitta ma lamarin Allah da son zuciya ko ka yi kari cikin addinin Allah da bidi'a ko ka yi shakka a cikin nassoshin addini wanda zai kai ga ture su ko kuma yi tawilin su.

Daga karshe liman ya yi maganar matattun zukata masu kin maganar Allah da zukata masu rashin lafiya wadanda suke guje ma karantarwar gaskiya da kin aikata ta.

Sannan ya rufe da Hadisin Huzaifa wanda ya yi maganar fitinu kuma ya ba da mafita.

Liman ya yi addu'oi masu yawa masu albarka musamman ga Alhazai da wadanda suka yi masu hidima da musulmin da ke cikin tashin hankula a Arakan da sauran wurare.

Allah ya amsa.

Share this


0 comments:

Post a Comment