Idan Saki Ya Fito Daga Baki Ba Ya Komawa!!! Dr Jamilu Yusuf Zarewa
Tambaya

Assalamu alaikum malam wata baiwar Allah ce suka sami sabani da mijinta sai ya bita inda take aiki yaje yana nemanta sai ta fadama wata agurin taje tacemai batanan sai mijin yace da 'yar sakon tace ya saketa saki uku kuma itama taji da kunnenta, sai daga baya yace shi be saketa ba,  shine tace atambaya mata ta saku ko aurensu nanan tunda ba ita yafada ma ba.Nagode

Amsa
Wa alaikum assalam, Ta saku mana tun da saki ba'a wasa da shi in har ya fito daga baki  ko da wasa ne ba ya komawa, tun da ya zartu kamar yadda hadisi ya tabbatar da hakan,  musamman kuma wacce aka yiwa sakin ta ji da kunnanta, ai karya ta kare.
Inkarinsa ba zai yi amfani ba, tun da an tabbatar ya furta.

Don neman karin bayani duba: Zadul-ma'ad 5/204.

A mazhabarmu ta Malikiyya ta saku saki uku, amma akwai malaman da suke ganin za'a bar shi a saki daya, tun da saki uku A kalma daya Bidi'a ne, kuma haka  ake hukuntawa a zamanin Annabi S.A.W. da zamanin Abubakar RA da wani bangare na zamanin Umar RA, kamar yadda hadisin Ibnu Abbas ya tabbatar da hakan

Allah ne mafi sani.

Dr, Jamilu Zarewa

16/09/2017

Share this


0 comments:

Post a Comment