Watan ALLAH Mai Alfarma (Almuharram) Sheikh Ibrahim Daurawa Kano


WANAN WATAN YANA KUNSHE DA ABUBUWA NA ALKHAIR, MASU YAWA, DAGA CIKI:
NA DAYA' AN KIRAWO SHI WATAN ALLAH MAI ALFARMA .
MANZON ALLAH SAW YACE, WATAN ALLAH ALMUHARRAM, SAHIHU MUSLUM.
NA BIYU, YIN AZUMI A CIKIN SA, YAFI KO WANNE AZUMIN NAFILA LADA, MAFI DARAJAR AZUMI BAYAN RAMADAN SHINE WATAN ALLAH ALMUHARRAM, SAHIHU MUSLUM
NA UKU, AKWAI AZUMIN RANAR ASHURA, MANZON ALLAH SAW YACE, INA FATAN AZUMIN ASHURA YA KANKARE ZUNUBIN SHEKARA GUDA DATA GABATA. SAHIHU MUSLUM
NA HUDU. YIN AZUMIN RANAR TASU'A, ANNABI SAW YAYI NIYAR AZUMIN TASU'A,
NA BIYAR, ACIKIN WANNAN WATA, ALLAH YA HALAKAR DA FIR'AUNA, YA TSERATAR DA ANNABI MUSA DA JAMA'ARSA
NA SHIDA, A RANAR GOMA GA WATAN, JIKAN MANZON ALLAH SAW, SAYYADINA USAINI, YAYI SHAHADA.

MALAMAI SUNYI MAGANA BIYAR AKAN YADDA ZAAYI AZUMIN ASHURA.
NA DAYA : AYI AZUMIN RANAR TARA KAWAI
NA BIYU : AYI AZUMIN RANAR GOMA KAWAI
NA UKU : AYI AZUMIN RANAR TARA DA GOMA
NA HUDU : AYI AZUMIN RANAR TARA DA GOMA DA SHA DAYA
NA BIYAR : AYI AZUMIN RANAR GOMA DA SHA DAYA.
ABINDA YAFI SHINE: AZUMIN TARA DA GOMA SABODA ANNABI SAW YAYI NA GOMA, KUMA YAYI NIYAR NA TARA.
ALLAH YA AMSA MANA.
KUMA KADA A MANTA DA AZUMIN KWANAKIN HARKE WATO SHA UKU SHA HUDU SHA BIYAR.

AKWAI BIDIO'I MARASA ASALI DAGA CIKI
A, CIKA CIKI.
B, LARABGANA.
C, ADDUA SABUWAR SHEKARA.
D, ZAMAN MAKOCI,
E, SANYA BAKAKEN KAYA .
F , SHAN RUWAN RIJIYA BAKWAI
G, SANYA ALLURA BAKWAI ACIKIN ZARE
H, AJIYE JELA DOMIN YIN ABINCIN CIKA CIKI.
DA MAKAMANTANSU,
ALLAH YA BAMU SAA DA DACEWA DA SUNNAH.

Share this


0 comments:

Post a Comment