Yawan Riya A Aikin Hajji Da Umara Dr Muhammad Sani Umar R/lemo


Imam Al-qarafi yana cewa: "Allah Ta'ala ya ce: (Kuma ku cika ayyukan Hajji da Umara saboda Allah), watau ya kara da fadar: (saboda Allah), amma bai fadi irin haka ba ga Salla da makamancita, dalili kuwa shi ne, yawaitar riya sosai a cikin aikin Hajji da Umara. Bibiyar halayen jama'a ya nuna gaskiyar hakan, domin ta kai cewa, da yawa daga cikin alhazai idan wani ya ji an fadi wani labari, to da wuya a wuce bai ce shi ma irin haka ya faru da shi ko da wani ba lokacin da suke aikin Hajji. To saboda kasancewar Hajji da Umara ayyuka ne da ake yawan samun riya a cikinsu ya sa Allah ya kara da cewa: (saboda Allah). Duba, Az--Zakheerah, juzi'i na 3, shafi na 173.

Share this


0 comments:

Post a Comment