ADDU'AR SAMUN DUKIYA DA 'YA'YA MASU ALBARKAWannan addu'ar an tsagota ne daga shahararriyar addu'ar nan wacce Manzon Allah (saww) yayi ma Sayyiduna Anas bn Malik (ra) alokacin da Mahaifiyarsa ta kawoshi gareshi.

Ga addu'ar nan kamar haka :

اللهم أكثر مالي وولدي وبارك لي فيما أعطيتني.

ALLAHUMMA AKTHIR MALIY WA WALADIY, WA BARIK LIY FEEMA A'ATAITANEE.

FASSARA : "Ya Allah ka yawaita dukiyata da 'ya'yana. Kuma ka albarkaceni acikin abinda ka bani".

ADUBA :

Sahihul Bukhariy hadisi na 1982.
Sahihu Muslim Hadisi na 660.

BAYANI
********
Albarkacin wannan addu'ar da Manzon Allah (saww) yayi ma Sayyiduna Anas bn Malik (ra), Sai da Sayyiduna Anas ya rayu kusan shekaru ɗari (100) aduniya. Kuma da idonsa sai da yaga fiye da ƴaƴa ɗari  daga cikin zuriyarsa.

Hakanan sai da ya zamanto dukiyarsa tayi albarka ta yawaita sosai. Har ma bishiyoyin dabinon gonarsa sau biyu suke haihuwa duk shekara.

Don haka Zauren Fiqhu yake jan hankalin ƴan uwa cewa mu riƙe irin waɗannan addu'o'in da muhimmancin gaske. Domin hakika Allah yana yin azaba ga wadanda basu yin addu'a. Kamar yadda kuma yake yin ni'ima da ɗaukaka da rufin asiri ga bayinsa masu yawan addu'a.

Zauren Fiqhu yayi izini ga dukkan ɗalibai cewa zasu iya tura wannan addu'ar ga dukkan Musulmai domin su amfana (Ba tare da editing ba).

Amma muna ƙara jan hankalin ɓarayin fasaha cewa suji tsoron Allah su dena idan har su Muminai ne. Allah yasa mu dace.

DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP 10-01-1438 (12-10-2016).

Share this


0 comments:

Post a Comment