Alkur'ani Maganar Allah ce Kuma Wahayin Shi Dr Ibrahim Jalo Jalingo


1. Ba a siffanta Alkur'ani Mai girma da cewa: Shi halitta ce, ko kuwa shi mai halitta ne ba, a'a abin da ake cewa game da shi shi ne: Alkur'ani Mai girma magana ce ta Allah, kuma wahayi ne naSa, wannan shi ne mazhabar Magabata; Imam Malik da waninsa.

2. Imam Husain Al-Bagwiy ya ce cikin littafinsa Sharhus Sunnah 1/186:-
((وقد مضى سلف هذه الأمة وعلماء السنة على ان القرءان كلام الله ووحيه ليس بخالق ولا مخلوق، والقول بخلق القرءان ضلالة وبدعة لم يتكلم بها احد في عهد الصحابة والتابعين رحمهم الله)).
Ma'ana: ((Magabatan wannan Al'ummah tare da Malaman Sunnah sun tafi a kan cewa: Alkur'ani Maganar Allah ce kuma wahayin Shi, sam ba mai halitta ba ne ba kuma wanda a ka halitta shi ba ne. Maganar cewa Alkur'ani halitta ce bata ce, kuma bidi'ah, babu mutum daya a zamanin Sahabbai da Tabi'ai Allah Ya yi musu rahama da ya taba hurta wannan maganar)).

3. Imamul Baihaqiy ya ruwaito cikin Sunan Athari na 21,415 daga Yahya Bin Khalaf Al-Muqri ya ce:-
((كنت عند مالك بن أنس، فجاءه رجل فقال: ما تقول فيمن يقول: القرءان مخلوق؟ فقال: زنديق كافر فاقتلوه)).
Ma'ana: ((Na kasance a gurin (Imam) Malik Dan Anas, sai wani mutum ya zo ya ce: Me kake cewa game da mutumin da yake cewa: Alkur'ani halitta ce? Sai (ya amsa) ya ce: Zindiki ne kafuri ku kashe shi)).

4. Imamuz Zahbiy ya ce a cikin littafin "Mukhtasarul Uluwwi Lil Aliyyil Gaffar" shafi na 75: Maimuun Bin Yahya Al-Bakriy ya ce:-
((قال مالك: من قال القرءان مخلوق يستتاب فان تاب وإلا ضربت عنقه)).
Ma'ana: ((Malik ya ce: Duk wanda ya ce Alkur'ani halitta ce, to a neme shi da ya tuba, in ya tuba shi ke nan, in kuma bai tuba ba sai a sare wuyansa)).

Allah muke roko da Ya tausaya mana Ya tsare mu daga fadawa cikin bidi'o'in Mu'utazilawa, da ma sauran bidi'o'in. Ameen.

Share this


0 comments:

Post a Comment