Aqidar Imam Ahmad Itace: Alkur'ani Maganar Allag ce Ba Hallitta Ba

Aqidar Imam Ahmad Bin Hambal wanda ya rasu a shekarar Hijira ta 241 game da Alkur'ani Mai girma shi ne: Shi Alkur'ani maganar Allah ce ba halitta ba ne.
Hujja:-
Imam Abubakar Al-Khallal wanda ya rasu a shekarar Hijira ta 311 ya ce a cikin littafinsa As-Sunnah Athari na 1796:-
((اخبرنا محمد بن علي، قال: حدثنا مثنى بن جامع، قال: قلت لاحمد بن حَنْبَل: اي شيء تقول في القرءان؟ قال: كلام الله وهو غير مخلوق. قلت: ان بعض الناس يحكي عنك انك تقول: كلام الله وتسكت! قال: من قال ذَا فقد ابطل)).
Ma'ana: ((Muhammad Bin Ali ya ba mu labari ya ce: Muthannaa Bin Jaamee ya tada mana ya ce: Na ce wa Ahmad Bin Hambal: Wani abu ne za ka ce game da Alkur'ani? Sai ya ce: Maganar Allah ce shi ba halittacce ba. Sai na ce: Sahin mutane na hikaitowa daga gare ka cewa kana cewa: Alkur'ani maganar Allah ce sai kuma ka yi shiru.  Sai ya ce: Duk wanda ya fadi wannan lalle ya yi karya)).

Shi ma Imam Ibnu Baddah Al-Ukbariy wanda ya rasu a shekar Hijira ta 387 ya ruwaito irin wannan magan daga shi Imam Ahmad Bin Hanbal Allah Ya yi masa rahama a cikin littafinsa mai suna Al-Ibaanatul Kubraa 5/308.

Ke nan Imam Ahmad Bin Hanbal ba Waaqifiy ba ne cikin mas'alar Alkur'ani kamar yadda wasu 'yan bidi'ah ke ikirari. Allah Ya taimake mu. Ameen.

Share this


0 comments:

Post a Comment