Audio :- Muhadarra Bbc Hausa Da Muhammad sani Umar R/lemo


Wani malamin musulunci a Najeriya ya kalubalanci ikirarin cewa kasar Saudiyya na koyar da fannonin ilmi da ke rura wutar tsaurin ra'ayin addinin musulunci a duniya, inda ya ce da gaskiya ne wannan zargi to da yanzu duniyar ma ba za ta zaunu ba saboda yawan masu zafin ra'ayi.
Dr. Muhammadu Sani Umar Rijiyar Lemo malami a Jami'ar Bayero Kano wanda kuma ya yi karatun digirinsa na farko har zuwa na uku a Saudiyya ya yi ikirarin cewa Allah ya yi yawa da daliban da kasar ta yaye a duniya, kuma da tsattsauran ra'ayin addini suka koya "da yanzu duk mu ma mun zama 'yan ta'adda".

"Muna nan irinmu ba iyaka. Ba na jin akwai wata kasa da ta yaye dalibai na ilmi wadanda suke karantarwa kamar Saudiyya, in ji shi."
Ya ce yanzu idan ka dubi wadanda ake fama da su a nan kasar ('Yan Boko Haram), dalibi nawa ne aka ce maka daga Saudiyya yake? Wane ne a cikinsu ya je Saudiyya ya yi karatu?
Domin sauraren hirar da bbchausa tayi da malamin sai ka latsa nan
Share this


0 comments:

Post a Comment