Bambanci Tsakanin Kabli Da Ba'adi


1. SUJJADAR KABLIYA:- Ana yin ta ne kafin sallama. Bayan mutum ya yi tahiya, kafin ya yi sallama, sai ya sake yin wasu sujjadu guda biyu, sannan ya sake yin wata tahiyar, Sannan ya yi sallama. Wannan ita ce Sajjadar Kabaliya.

Dalilan da suke sawa ayi ta:- Idan mutum ya yi ragi a cikin Sallarsa, ko kuma ya tauye wasu sunnoni Karfafa guda biyu ko sama da haka. (atakaice kenan).

YADDA AKE YINTA:- Ana yin ta ne bayan an yi tahiya kafin sallama, sai a sake yin wasu sujjadu‎ guda biyu, sannan a yi tahiya a yi sallama.

2. SUJJADAR BA'ADIYA:- Ana yin ta ne yayin da aka kara wani abu a cikin Sallah. Ko kuma yayin da mutum ya mance da wata farillah, ko kuma rukuni daga cikin sallar sa.‎ Bayan ya kawo wannan farillar da ya mance, to sai yayi sujjada Ba'adiya.

Dalilan da suke sawa ayi ta:- Idan mutum yayi kari a cikin Sallarsa, ko kuma yayi dogon tunani a cikin sallarsa ta yanda bai iya tuna raka'o'i nawa ne yayi. (atakaice kenan).

YADDA AKE YINTA:- Ana yin ta ne bayan an yi tahiya an yi sallama, sai a sake yin wasu sujjadu‎ guda biyu, sannan a yi tahiya a yi sallama.

(WALLAHU A'ALAM).

Rubutawa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Share this


0 comments:

Post a Comment