Bin Ka'idojin Hukumar Zabe Ba Zai Cutar Da Mu Ba Sai Dai Ya Amfane Mu Dr Ibrahim Jalo Jalingo

1. Mu ke da rinjaye a Jihar Taraba; saboda haka matukar dai 'yan Taraba suka yi rajistan zabe a bisa ka'aidar da Hukumar zabe ta bayyana, suka kuma fito kwansu da kwarkwatarsu suka jefa kuri'arsu a bisa ka'ida, aka kuma kirga dukkan kuri'ar da aka jefa to kuwa lalle mu ke tsammanin samun nasara ba wai wasunmu ba.

2. Masu lura da yadda al'amura ke tafiya sun fahimci irin yadda azzaluman da suke son share al'ummarmu daga dukkan wani muhimmin hakki nasu suke kawo wasu mutane daga bangarorin wasu jihohi da ke makwabtaka da mu domin su yi rajistar zabe a wasu sassa na kananan hukumomin wannan jiha tamu watau Taraba, suke kuma kawo yaran da ba su kai shekarun yin rajista ba domin a musu rajistar; saboda kawai su sami nasarar zabe ko ta halin kaka idan shekarar zabe ta zo!

3. Muna jinjina wa INEC a kan dukkan matakan da ake gani take dauka domin tabbatar da bin doka da oda a cikin dukkan wani al'amari da ya shafi zaben 2019 da muke fiskanta.

4. Muna kira ga dukkan al'ummarmu mazansu da matansu cewa duk wanda ya isa mallakar katin zabe amman kuma ba yi da ita to ya gaggauta zuwa gurin rajistan zabe domin a yi masa rajista, sannan ya fito ya yi zabe idan ranar zabe ta zo. Allah Ya taimake mu. Ameen.

Share this


0 comments:

Post a Comment