Duk Surutan Da Awaam Ko Mahassada Ke Yi Game Da Izala Ba Su Da Wata Kima A Idanun Doka Dr Ibrahim Jalo Jalingo


1. Jama'atu Izalatil Bid'ah Wa Ikamatis Sunnah kungiya ce mai constitution da kuma rajistan Gwamnatin Nigeria. Duk wanda ke son sanin tarihinta da kuma tsarin gudanar da al'amuranta sai ya je ya karanci constitution dinta. Babu wani al'amari muhimmi da ya shafe ta face an bayyana shi a cikin wannan constitution din nata.

2. Kuma dukkan membarta matukar dai ba yaudarar kansa yake yi ba to kuwa dole ne ya lazimci constitution dinta da aka gina a kan Alkur'ani da Hadithi da kuma Ijma'i a duk lokacin da zai tafiyar da wani al'amari nata; saboda fadar Manzon Allah mai tsira da amincin Allah a cikin ingantaccen hadithinsa: "Musulmai suna kan sharuddansu ne".

Allah Ya taimake mu a kan yin riko da Sunnar AnnabinSa har kullum. Ameen.

Share this


0 comments:

Post a Comment