Fatawar Rabon Gado (138) Dr Jamilu Yusuf Zarewa


Tamabaya

Assalamu Alaikum, Malam yaya za a raba gadon iyalan da suka mutu a hadarin mota kuma ba a san wanda ya riga wani mutuwa ba? Menene raayin mazahabobi akan hakan? Nagode

Amsa

Wa alaikum assalam, Ra'ayin mafin yawan malamai shi ne babu gado a tsakaninsu, saboda daga cikin sharudan gado shi ne: tabbatar da rayuwar magaji bayan wanda zai gada ya mutu, a nan kuma ba'a tabbatar ba.

Don neman karin bayani duba: Attahakikatu Al-mardhiyya shafi na (240)

Allah ne mafi sani

Amsawa

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
26/09/2017

Share this


0 comments:

Post a Comment