Fatawar Rabon Gado(142) Dr Jamilu Yusuf Zarewa


Tambaya

Assalamu alaikum, malam matace ta rasu ta bar yan uwa li'ummai da kuma Dan uwa li'abbi shi kadai ba Da ba iyaye ba kowa sai su, to ya gadon zai zama?

Amsa
Wa alaikum assalam, za'a raba dukiyar kashi uku, kashi daya a bawa li'ummai su raba daidai babu bambanci tsakanin mace da namiji, ragowar kuma sai a bawa li'abi ya cinye.

Allah ne mafi sani

Dr, Jamilu Zarewa

13/10/2017

Share this


0 comments:

Post a Comment