Hattara Dai! Kar Ka Zama Cikin Wadannan!!!


Imam Ibnul Kayyim (Allah Ya Jikansa Da Rahama) Yana cewa "Abin mamaki, sai ka ga mutum yana yi masa sauki ya kiyayi cin haramun, da zalunci, da zina, da sata da shan giya da kallon haramun da makamantansu, amma kiyaye harshensa yana masa wahala, har sai ka ga mutumin da ake nuna shi wajen addini da gudun duniya da ibada, amma yana fadin kalmar dake jawo fushin Allah, ba tare da ya damu ba, kalmar da zata sauko da shi kasa fiye da nisan da yake tsakanin gabas da yamma.

Sau da yawa zaka ga mutum mai tsantseni wajen barin alfasha da zalunci amma harshensa yana cikin kage a cikin mutuncin rayayyu da matattu amma bai damu da abin da yake fada ba" (Aljawabul Kafi 203). Don haka dan uwa musulmi ka rika lura da abin da zaka furta da wanda zaka rubuta, Allah YaSa Mu Dace.

Share this


0 comments:

Post a Comment