Jahilcin Jingirawa Da Hayaniyarsu


1. Yana daga cikin jahilci tare da hayaniyar Jingirawa abin da suka dauka na cewa: Dukkan Majalisai goman nan da suke cikin constitution din Kungiyar Izala majalisu ne na jahilai in banda Majalisar masu wa'azi, ita wannan ita ce kadai ba ta jahilai ba!! Kuma wannan jahilci da son zuciya da yarfe nasu su ne suka kai su ga yi wa  jagorancin kungiyar Izala tawaye, da kuma yi wa tsarin mulkinta watau construction dinta tawaye!!

2. Tabbas dalilin wannan jahilci da son zuciya da yarfe nasu ne ya sa suka fada cikin bata daban daban; batar farko ita ce irin yadda lazimin wannan mataki nasu ya maida M. Isma'ila Idris wani irin sakaran jahili wanda bai san abin da yake yi ba; tunda dai shi ne ya shugabanci kwamitin rubuta wa kungiyar Izalah constitution dinta din; a inda ya yarda aka yi mata majalisu goma (da na agaji sha daya) amma kuma goma daga cikinsu dukkansu majalisun jahilai ne!!

3. Su Jingirawa sun kamanta kawunansu, sun kuma kamanta tsarin kungiyarsu ta Jingiranci da tsarin bidi'ar Shi'ah ta Wilaayatul Faqeeh da Ayatullahi Khomainiy ya kirkiro wa 'Yan Shi'ah a Kasar Iran a inda shugaban Majalisar malamai ta Yan Shi'ah shi ne ke mulkan Kasar Iran mulki na hakika, amma shi shugaban Kasa da sauran majalisu da ake da su a tsarin mulkin Kasar mulkinsu mulki ne kawai Suuriy.

4. Abin mamaki Jingirawa duk da yake sun yi wa shugabanci da kuma tsarin mulkin kungiyar Izalah tawaye, sun koma sun ari bidi'ar Ayatulkahi Khomainiy ta Wilaayatul Faqeeh, to kuma sai ga shi maimakon su nemi wani malami masani su nada shi a matsayin shugabansu; watau shugaban kungiyarsu, a'a sai ga shi sun je sun kawo wani jahili murakkabi a matsayin shi ne shugaban nasu!!

5. Domin su Jingirawa su kara bayyanar da kamantuwarsu da Khominiyaawa sai ga shi kamar yadda shi Ayatullahi Khomainiy ya kirkiro wa 'Yan Shi'ar Iran mukamin abin da ya kira Wilaayatul Faqeeh wanda babu shi a asalin tsarin bidi'ar Shi'ah haka nan su ma Jingirawa suka kirkira wa tsarin kungiyarsu ta Jingiranci wani mukami mai suna "Shugaban gudanarwa"; domin wannan kalma ba a ambace ta ba ko da a guri guda ne a cikin constitution din Kungiyar Izalah, amma sai ga shi ta zama cikin shahararrun kalmomi cikin kungiyar Jingiranci!!

Allah Ya tsare mu da sharrin bidi'ah da kuma sharrin hawaa. Ameen.

Share this


0 comments:

Post a Comment