kasan Kanka Da Kanka Tambayoyi (50) Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Muna cikin wani zamani, da mutane, sunfi damuwa da bayani akan wasu fiye da kansu, sunfi binciko laifin wasu fiye da nasu, Sayyadina Umar Yace kuyi kanku hisabi kafin ayi muku, Abubawan da suke jawo tsira, Bautawa Allah shi kadai da iklasi, akan sunnar Manzon Allah, a cikin Akida, da Ibada, Da mu'amalah, da Halaye masu kyau, yi kanka tambaya, hamsin don kasan matsayinka :
Allah yasa mu dace :
1- waye ya yika ?
2- mai yasa ya yika ?
3- kai waye ?
4- A ina kake ?
5- mai kake yi ?
6- Ina zaka ?
7- mai zai faru ?
8- mai kafi so a rayuwarka ?
9- mai kafi ki rayuwarka?
10- Duk abinda kakeyi, kana da hujja a sharia?

11- su waye abokanka?
12- Yaya zamanka da iyayanka?
13- Yaya zamanka yake da iyalanka?
14- Wace kungiya kakeyi don me?
15- A kwai wani yanzu haka da bakwa shiri da shi?
16- Tsakaninka da Allah ka taba cin amanar wani?
17 Kanayin karya?
18- Kana Dun guma ashariya?
19- Yaya zamanaka da makotanka?
20- Wace shedar ilmi kake dauke da ita?

21- kana salloli a Jam'i musamman a masallaci?
22- yaya alakar ka da danginka take ?
23- shin kana sada zumunta?
24- shin kana bayar da sadaka ?
25- shin kana karanta Alkur'ani mai girma?
26- kana azumin litinin da Alhamis?
27- kana sallar Shafi'i da wuturi?
28- kana zuwa asibiti domin ziyarar marasa lafiya?
29- Kana yawan saba alkawari ?
30-shin kana azumtar kwanaki masu haske,
ranar sha uku, sha hudu, sha biyar?

31- shin kana kiyamul- laili?
32-kana umarni da kyakyawa da hani da mummuna?
33- kana zuwa aiki akan kari kuma ka tashi akan lokaci?
34- kana zuwa gaban malami domin daukar karatu?
35-ka tabbatar abinda kake ci halal ne?
36- kana kuwa damuwa da halin da yan uwanka musulmi suke ciki?
37- kana taimaka marayu kuwa?
38- salati nawa kake yiwa Annabi saw kullum?
39- Istigfari nawa kakeyi kullum?
40- kana zuwa makabarta domin tuna lahira?

41- kana zuwa taaziyya da sallar Jana'iza?
42- ka taba yin kuka saboda tsoran Allah?
43- shin kana yiwa dukkan musulmi sallama ko kuwa sai wanda ka sani?
44- kanayin rantsuwa akan karya kuwa?
45- kana shan taba ko wiwi ko giya ko hodar iblis?
46- kana jin kade- kade, da wake- wake?
47- kana aske gemunka?
48- ka taba karbar cin hanci?
49- kana kyautawa iyalanka?
50- kana gaba da wani kuwa?

Allah kasa mu dace, kuma Allah Ya shiri my gaba daya. Ameen Ya Allah

Share this


0 comments:

Post a Comment