Saudiyya Bata Koyar Da Ta'addaci ! Sai Dai Tauheed Da Riko Da Sunnah Tsantsa!!! Dr Abdallah Usman Umar G/kaya


A satin daya gabata Gidan redion BBC Anyi hira da wani Bawan Allah a matsayinsa na daya daga cikin limamai na national Mosque Abuja , akan ya fadi  raayinsa akan wata gagarumar Cibibiyar Kulawa da Tattaro dukkan Hadisan manzon Allah saw a kasar, kamar yanda Hukumar saudiyya din tayi babbar madaba,ah ta Sarki malik fahad Allah yajikansa  a madina dake Buga Qur,anai, a ke rabasu a duk fadin duniyar nan, don haka ake so Sunnahr Annabi saw ma ayi mata irin wannan Gata.

@ Tun ba yau ba malamai masana a fadin Duniyar nan suke kira ga kasar saudiyya din don samar da wannan gagarumar Cibiyar, kuma ta amsa yin hakan a cikn wannan watan. Amma sai gashi wassu sun canza manufar wannan Zance  sun juya maanar suna gayawa Duniya cewa an samar da wannan cibiya ne don Share wassu Hadisai da suke koyar Da tsatsauran raayin Adddinin musulunci, SUBHANALLAHI!!

@ Akwai abun mamaki matuka gama garin dan musulmi kadai ya budi baki ya danganta wannan kasa mai Tsarki kasar Manzon allah Kasar wahayi, ALKITABU WAS SUNNAH, da Taadanci, ballanta na mutumin da yake danganta kansa ga Malunta , kuma limami a babban masallacin kasar Nigeria National Mosque, ya aikata wannan katobara! Subhanallahi.

@ Shi wannan limami ya danganta samar da wannan cibiyar , cewa wai kokari ne, na kasar don sasauta Tsatsauran raayi da Taadaanci da kasar tayi suna akan karantar da mutane, da kuma kyautata alakar ta da kasa shen turawa, subhanallahi!!! Wannan magana tayi muni , wajibi ne malamin ya janye wannan lafazi marar maana ko Tushe.

ILLOLIN WANNAN TUHMA DA BATANCI SUNE
1. Wannan yana nuna wannan Limami zai haddasa Gaba da rashin Jituwa da lalata huldar jakadanci tsakanin kasar saudiyya da Nigeria.
2. A matsayinsa na limami a babbabn masallacin kasa ya fito Duniya a Radio BBC ya jefi wata kasa da koyar da Taadanci.? Wannan magana tana da Hatsari matuka akansa da kuma alakar kasashen guda biyu.
3. Ko shakka babu idan wakilan kasar saudiyya a nigeria sukaji wannan kazafi zasu iya daukar mummunan mataki na Tafka shi a kotu, daga baya hakan yasa yayi hasarar Mutuncin sa a idon mutane.
4. Wannan magana fada ne karar da Daawar sunnah da kiran akan Tauheed, da kuma jifan Malaman da sukayi karatu a saudiyyar da sun koyo taadanci.
5. Haka yana nuna butulci ga irin hidimar da kasar ke yiwa addinin musulunci da masallatan nan guda biyu na makka da Madina da daukar Dalibai karatu kyauta,da takeyi kulum a fadin Duniyar nan!

FADA DA DAAWAR TAUHEED DA KIRA GA SUNNAH BAZAI KAIKA GA KOMI BA SAI HALAKA . ALLAH YA NUANA MANA GASKIYA, YA KUMA HADAKAN MUSULMI AKAN ALKITABU WAS SUNNAH !

Share this


0 comments:

Post a Comment