Shin Kai Da Dukiyarka Na Babanka Ne? Dr Jamilu Yusuf Zarewa


Tambaya

Assalamu Alaikum Dr.
 Tambaya ta itace: menene hukuncin   mahaifin da ya cinye sadakin 'yasshi da kudaden aure gaba daya , ba gado ba kujeru,  bai mata  komai na kayan aure ba,  bai kuma biyata kudadentaba, wai Don mijin 'yaqi kawo akwatin 'yar agani alhali kuma yasamu yaqinin cewa anyi akwatin.

Amsa
Wa alaikum assalam,

 Annabi S.AW. yana cewa: (Kai da abin da ka mallaka na mahaifinka ne) kamar yadda Ibnu Majah ya rawaito a hadisi mai lamba ta: (2291) da kuma Ibnu Hibban a Sahihinsa 2/142.

 Malamai sun yi karin haske game da wannan hadisin inda suke cewa Ya halatta Uba ya ci dukiyar 'dansa ko 'yarsa da sharuda guda uku:

1.Idan Dan ba ya tsananin bukatar abin.

2. Idan ba wani ya bawa kyauta ba, shi ya yi amfani da shi.

3.Idan bai zama a rashin lafiyar mutuwar daya daga cikinsu ba.

A bisa sharudan da suka gabata,. za mu fahimci abin da Uban ya yi bai dace ba, tun da 'yarsa tana tsananin bukatar abin da ka ambata na Gado da kujeru da sauransu.
Allah ne mafi sani

Dr, Jamilu Zarewa

25/09/2017

Share this


0 comments:

Post a Comment