Yana Rubuce Cikin Litttattafan Shi'ah Cewa Su ne Suka Kashe Hussaini R.A Dr Ibrahim Jalo Jalingo1. Yana rubuce a cikin littattafen Shi'ah cewa: su 'yan Shi'ah su ne suka kashe Sayyidina Husaini -Allah Ya kara masa yarda- ba wai wasun Shi'ah ba. To amma da yake bidi'ar Shi'ah da ma ta ginu ne a kan nisantar gaskiya, da lazimtar hayaniya, da yarfe sai ga shi a yanzu sun dora wa wasunsu kisan wannan bawan Allah Sayyidina Husaini Dan Sayyidina Aliyyu Allah Ya kara musu yarda.

2. Ya zo cikin littafin Al-Ihtijaaj na Tabarisiy 32/2, da littafin Al-Malhuf na Ibnu Taawus shafi na 92, da littafin Muntahal Aamal na Abbas Al-Qumiy 1/572, da littafin Lawaa'ijul Ash'jaan na Al-Ameen shafi na 158, da littafin Rihaabu Karbalaa na Husain Kuuraaniy shafi na 183, da littafin Maqtalul Husain ba Abdurrazzaq Al-Maqram shafi na 317, da littafin Tazallumul Zahraa na Radhiyyul Qazweeniy shafi na 262, da littafin Maqtalul Husain na Murtadhaa Ayyad shafi na 87, dukkan wadannan sun ruwaito daga Dan Sayyidina Husaini mai suna Aliyyu Zainul Aabideen cewa ya ce:
((أيها الناس ناشدتكم بالله هل تعلمون انكم كتبتم الى ابي وخدمتموه واعطيتموه العهد والميثاق والبيعة وقاتلتموه وخذلتموه، فتبا لما قدمتم لانفسكم وسواة لرأيكم بأية اعين تنظرون الى رسول الله صلى الله عليه واله وسلم اذ يقول لكم: قتلتم عترتي وانتهكتم حرمتي فلستم من امتي)).
Ma'ana: ((Ya ku mutane! Ina gama ku da Allah, ko kuna sane da cewa lalle ku kun rubuta wa mahaifina kuka yaudare shi, kuka danka masa Alkawari da Mubaya'ah, kuka yake shi, kuka kaskantar da shi. Tir da abin da kuka gabatar wa kanku, tir da munin ra'ayinku. Da wasu irin idanu ne za ku rika kallon manzon Allah Allah Ya yi masa tsira da amincin tare da iyalansa a lokacin da zai ce da ku: Kun kashe iyalan gidana, kun ci mutuncina. Ba kwa daga cikin al'ummata)).

3.  Babban malamin Shi'ah mai suna Muhsinul Ameen ya ce a cikin littafinsa mai suna A'ayaanush Shi'ah 1/26:-
((ثم بايع الحسين من أهل العراق عشرون ألفا غدروا به، وخرجوا عليه وبيعته في اعناقهم فقتلوه)).
Ma'ana: ((Sannan mutum dubu ishrin daga cikin mutanen Irak suka yi wa Husaini mubaya'a, suka yaudare shi, suka yi masa tawaye alhalin mubaya'arsu tana kan wuyayensu, suka kuma kashe shi)).

4. Ibnu Taawus ya ruwaito cikin littafinsa Malhuuf shafi na 86, da Murtadhaa Ayyad a cikin littafinsa Maqtalul Husain shafi na 83, da Radhiyyul Qazweeniy a cikin littafinsa Tazallumuz Zahraa shafi na 257, dukkan wadannan malaman Shi'ah sun ruwaito cewa: A lokacin da Aliyyu Zainul Aabideen ya wuce wasu mutane cikin garin Kufah suna ta kuka suna ta kururuwa sai ya tsawata musu yana mai cewa:-
((تنوحون وتبكون من اجلنا فمن الذي قتلنا))؟
Ma'ana: ((Kuna kururuwa kuna ta kuka saboda mu, wane ne ya kashe mu))?

5. Irin wadannan maganganu an ruwaito su daga mutane da yawa daga cikin Ahlul Baiti kamar Ummu Kulthum diyar Sayyidina Aliyyu Bin Abi Taalib da sauransu. Allah muke roko da Ya taimaka wa al'ummarmu da suke cikin wannan mummunar bidi'ah ta Shi'ah ta yadda za su gaggauta barin ta ba tare da wani bata lokaci ba. Ameen.

Share this


0 comments:

Post a Comment