Fatawar Rabon Gado (145) Dr Jamilu Yusuf Zarewa


Tamabaya

Assalamu alaikum. Malam mutum ne ya rasu yana da mace daya da yara mata biyu da uwa da yayu biyu maza  da kuma mata hudu,  'yan'uwan uwarsu daya uba daya,  shin yaya rabon gadon sa zai  kasance? Allah ya karawa Dr. Lafiya da ilimi mai amfani

Amsa

Wa alaikum assalam, Za'a raba abin da ya bari gida: 24, a bawa 'ya'yansa mata kashi (16), matarsa kashi (3), mahaifiyarshi kashi (4), ragowar kashi dayan sai a bawa 'yan'uwansa su raba, duk namiji ya dau rabon mata biyu.
Allah ne mafi sani

Amsawa✍

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
20/10/2017

Share this


0 comments:

Post a Comment