FATAWAR RABON GADO (146) Dr Jamilu Yusuf Zarewa


*Tambaya*
Assalamu Alaikum Don Allah ina da fatawa akan mas'alar gado. Wata mata ce ta rasu, ba ta taba haihuwa ba amma ta bar kanwarta da suke uba daya, da kuma jikokin yayar ta. To kafin ta mutu, sai ta ce ta ba wa Wata 'ya da ta Rika gidanta. Ita kuma wannan 'yar ba ta da alaka ta jini da ita marigayiyar. To don Allah, ya ya lamarin raba gado zai kasance?

*Amsa*
Wa alaikum assalam, in har ta yi mata kyautar ne a lokacin tana cikin lafiyarta kyautar ta bayu, in kuma wasiyya ta yi to bai halatta ta wuce daya bisa ukun dukiyar da ta mallaka ba.

 Abin da ta bari sai a ba wa kanwarta ta cinye duka (Fardhan wa raddan).

Allah ne mafi sani
*Dr Jamilu Zarewa*
21-10-2017

Share this


0 comments:

Post a Comment