Fatawar Rabon Gado (149) Dr Jamilu Yusuf Zarewa

*Tambaya*

Assalamu alaikum, mallam Tambayar da za mu yi itace: mace ce ta rasu ta bar 'yarta mace ba ta da uwa ba uba, tana da 'yan uwa maxa da mata, a cikinsu akwai yan'uba da Wanda suka hada uwa da shi uba kowa da nasa, ya rabon gadanta yake? 
Allah ya sa ka alkhairi. 

*Amsa*
Wa alaikum assalam, Za'a raba abin da ta bari gida (6), a bawa 'Yarta kashi (3), 'yan'uwan da suka hada uwa kashi (2) su raba daidai, babu bambanci tsakanin mace da namiji..
Ragowar kashi dayan sai a bawa 'yan Uba su raba.

Allah ne mafi sani 

*Dr, Jamilu Zarewa*

02/11/2017

Share this


0 comments:

Post a Comment