Jinazah Ba Guri Ba Ne Na Gabatar DaHuduba Ko Yi Wa Jama'a Wa'azi Har Kullum :Dr Ibrahim Jalo Jalingo


1. Sunnah ce lokaci zuwa lokaci a sami wani wanda zai fadakar da wadanda suka halarci binne mamaci, amma ba zai dace da Sunnah ba a maida wa'azin tamkar wata lacca, ko a riki yin wa'azin a matsayin wani al'amari raatibi wanda sai an yi shi cikin ko wace jinazah.

2. Akwai hadithai biyu da suka tabbatar da cewa har sau biyu ne Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya yi wa Sahabbai jawabai na wa'azi -ba bisa siffar huduba ba- a inda ake binne wani mamaci. Hadithin farko shi ne wanda Aliyyu Bin Abi Dalib ya ruwaito kamar yadda ya zo cikin Sahihul Bukhariy Hadithi na 1362, da Sahihi Muslim Hadithi na 2647. Hadithi na biyu shi ne wanda Baraa Bin A'azib ya ruwaito kamar yadda ya zo cikin Musnad Ahmad Hadithi na 18534.

3. Kyamatar maida gurin binne mamata wurin yin jawabai masu kama da lacca, da kuma maida hakan al'amari raatibi da ake maimaitawa a duk lokacin da aka zo binne wani mamaci tabbas shi ne yake dacewa da abinda Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya zo da shi, shi ne kuma fahimtar da yawa daga cikin Malamanmu na Sunnah; kamar Sheikh Muhammad Bin Salihil Uthaimeen da wasunsa.
Allah Ya taimake mu Ya dora mu a kan yin daidai har kullum. Ameen.

Share this


0 comments:

Post a Comment