kada Tufar Musulmi Ta Wuce Idon Sawu Dr Ibrahim Jalo JalingoDuk inda Musulmi yake wajibi ne ya daure ya bi Allah a cikin suturar da yake sanyawa; watau wajibi ne ya tabbatar da cewa wandonsa, ko rigarsa, ko alkebbarsa ba su kasance kasa da idanun sawunsa ba. Wannan shi ne abin da Allah Ya wajabta masa a wannan babin.

Lalle ba daidai ba ne mutum musulmi a bisa zabinsa, da ganin damarsa, saboda kawai neman ado ya je ya biya tela kudi ya dinka masa Zunubi da Bala'I; watau: wandon da ya zarce idon sawunsa, ko rigar da ta zarce idon sawunsa, ko alkebbar da ta zarce idon sawunsa. Lalle wannan Bala'I ne babba cikin wannan Al'ummah Muhammadiyyah.

Imam Malik ya ruwaito Hadithi na 1,631 cikin Muwataa, da Imam Ahmad Hadithi na 11,023 cikin Musnad, da Abu Dawud Hadithi na 4,095 cikin Sunan, da Nasaa'iy Hadithi na 9,633 cikin Sunan, da Ibnu Majah Hadithi na 3,573 cikin Sunan, da Ibnu Hibban Hadithi na 5,447 cikin Sahih, da Dabaraaniy Hadithi na 13,113 cikin Muujam, da Ibnu Abi Shaibah Hadithi na 25,318 cikin Musannaf da isnadi sahihi daga Abu Sa'id Al-Khudriy ya ce: Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya ce:-
((ازرة المسلم الى نصف الساق، ولا حرج فيما بينه وبين الكعبين، ما كان أسفل من الكعبين فهو في النار، من جر إزاره بطرا لم ينظر الله اليه)).
Ma'ana: ((Suturar Musulmi zuwa tsakiyar kwabri ne, amma babu laifi cikin abin da ya kasance tsakaninsa da idanun sawu, abin da kuma ya kasance kasa da idanun sawu wannan shi yana cikin Wuta, wanda kuma suturarsa ta ja kasa saboda nuna ado sam Allah ba zai dube shi ba)).

Sayyidina Abubakar Allah Ya kara masa yarda ya kasance Idan ya dan gafala mayafinsa na jan kasa, Sannan nan da nan sai ya daga shi; kamar yadda Imam Ahmad da Baihaqiy suka ruwaito.

Saboda fa'idah ga wasu ayyuka da maganganun Sahabbai game da isbaalin sutura:-
روى الامام النسائي في السنن: ٩٦٢٠ عن ابن عباس رضي الله عنه قال: ((ان الله لا ينظر الى مسبل)).
وروى الدارمي في السنن: ٢٨١٠ عن عبادة بن قرط قال: ((إنكم لتأتون أمورا هي ادق في اعينكم من الشعر كنّا نعدها على عهد رسول الله صلى الله عليه وسلم من الموبقات. فذكر لمحمد يعني ابن سيرين فقال: صدق فارى جر الإزار من ذلك)).
وروى ابن ابي شيبة في المصنف: ٢٥٣٢٤ عن أنس بن مالك قال: ((الإزار الى نصف الساق أو الى الكعبين، لا خير فيما هو أسفل من ذلك)).
وروى ابن ابي شيبة في المصنف: ٢٥٣٢٦ ان عمر دعا بشفرة فرفع ازار رجل عن كعبيه ثم قطع ما كان أسفل من ذلك)).
وروى ابن ابي شيبة في المصنف: ٢٥٣٢٧ عن ابي إسحاق قال: ((رأيت ناسا من اصحاب رسول الله صلى الله عليه وسلم ياتزرون على أنصاف سوقهم؛ فذكر اسامة بن زيد، وابن عمر، وزيد بن أرقم، والبراء بن عازب)).
وروى ابن ابي شيبة في المصنف: ٢٥٣٣١ ان عثمان بن عفان كان إزاره الى نصف ساقيه، قال: فقيل له في ذلك؟ فقال: هذه ازرة حبيبي، يعني النبي صلى الله عليه وسلم)).

Allah Ka tausaya wa wannan Al'ummah Ka cusa mata ganin kyawun abin da duk yake sunna ce ta ManzonKa. Ameen.

Share this


0 comments:

Post a Comment