Magana Mai Matikar Kyau Dr Ibrahim Jalo Jalingo


Al-Haafiz Bin Rajab ya ce a cikin littafinsa mai suna: Al-Hikamul Jadiiratu Bil Izaa'ah shafi na 12:-
((فالواجب على من بلغه امر الرسول صلى الله عليه وسلم وعرفه ان يبينه للأمة وينصح لهم ويأمرهم باتباع أمره وان خالف ذلك رأي عظيم من الأمة فان امر رسول الله صلى الله عليه وسلم احق ان يعظم ويقتدى به من رأي اَي معظم قد خالف أمره في بعض الأشياء خطا)).
Ma'ana: ((Abin da yake wajibi a kan duk wanda umurnin Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya riske shi, ya kuma gane shi, to sai ya bayyana shi ga Al'ummah, ya yi musu nasiha, ya umurce su da bin umurnin shi; ko da hakan ya saba wa ra'ayin wani babba daga cikin Al'ummah; domin umurnin Manzon Allah mai tsira da amincin Allah shi ya fi cancantar a girmama a kuma yi koyi da shi a kan ra'ayin dukkan wani wanda ake girmamawa da ya saba wa umurninsa cikin sashin al'amura ta hanyar kure)).

Lalle wannan nasiha ce mai matukar muhimmanci. Allah Ya taimake mu. Ameen.

Share this


0 comments:

Post a Comment