Maganar Annabi Ta Yi Hannun Riga Da Maganar 'Yan Shi'ah Game Da Aisha Dr Ibrahim Jalo Jalingo
Maganar Manzon Allah mai tsira da amincin Allah game da Matarsa Nana A'isha Allah Ya kara mata yarda ta yi hannun riga da maganar 'yan Shi'ah masu muzanta ta da cin mutuncinta; wannan shi ne ya sa a lokacin da su batattun 'yan Shi'ah suke kafirta ta, suke la'antar ta, a lokacin ne kuma ita Shari'ar Musulunci ta bakin da ba ya karya watau Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ke siffanta ta da cewa ita Ahlul Baiti ce!

Imamul Bukhariy ya ruwaito Hadithi na 2637, da Imamu Muslim hadithin na 2770, da Imam Ahmad Hadithi na 25,664, da Imamul Baihaqiy Hadithi na 20,386 cewa: A lokacin da Jama'ar da  suka yi wa Nana A'isha kazafi da sharrin cewa ta yi zina, sai Manzon Allah mai tsira da amincin Allah:-
((فدعا عليا واسامة حين استلبث الوحي يستامرهما في فراق أهله، فاما اسامة فقال: اهلك ولا نعلم الا خيرا. وقالت بريرة: ان رأيت عليها أمرا اغمصه اكثر من انها جارية حديثة السن تنام عن عجين اَهلها فتاتي الداجن فتأكله. فقال رسول الله صلى الله عليه وسلم: من يعذرنا من رجل بلغني أذاه في اهل بيتي! فوالله ما علمت من اهلي الا خيرا، ولقد ذكروا رجلا ماعلمت عليه الا خيرا)).
Ma'ana: ((Ya kira Aliyyu da Usamah a lokacin da Wahayi ya yi jinkiin zuwa yana mai neman shawararsu game da rabuwa da iyalinsa; amma shi Usamah sai ya ce: iyalinka ce ita, kuma ba mu san wani abu ba in banda alheri. Bareerah kuwa sai ta ce: babu wani abu na nakasa da nake gani tare da ita in banda kasancewarta wata yarinya mai karancin shekaru wacce take barci ta bar kullun garin gurasa har awakin gida su rika zuwa suna cin sa. Sai Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya ce: Wane ne zai gamsar da mu har mu karbi uzurin mutumin nan da labarin cutarwarsa ga Ahlu baitina ya zo mini! Wallahi ni ban san wani abu ba game da iyalina in banda alheri. Tabbas sun ambaci wani mutum ni dai babu abin da na sani game shi in ba alheri)).

Allah Ya taimake mu har kullum. Ameen.

Share this


0 comments:

Post a Comment