Saurayina Yana Luwadi Menene Shawara Dr Jamilu Yusuf Zarewa


Tambaya

ASSALAMU ALAIKUM WA RAHMATULLAH. Malam Barka Da Asuba.
malam wata 'yar'uwammuce take tambayata tana da saurayi suna soyayya har an sa musu ranar aurensu amma yarinyar sai ta gano  saurayin aikinsa neman maza yan uwansa shine take tambayata ta rufa masa asiri suyi aure yahalatta??. Ahuta lafiya bissalam

Amsa

Wa alaikum assalam, Ta sanya a yi masa nasiha ko ita ta yi masa, in har  ya tuba, tuba ingantacce za su iya  yin aure, saboda wanda ya tuba daga zunubi kamar wanda bai taba aikatawa ba ne.

In bai tuba ba ana iya fasa auran saboda mai wannan aikin FASIKI ne, Annabi S.A.W. yana cewa: (Idan wanda kuka yarda da addininsa da dabi'unsa ya zo muku to ku aura masa) kamar yadda Tirmizi ya rawaito.

Mai neman maza dabi'unsa ba yardaddu ba ne, wannan ya sa za'a iya hana shi aure.
Sannan bai kamata a rufa masa asiri ba, musamman idan aka masa nasiha a asirce ya ki tuba saboda Mabarnaci ne.

In har za su yi aure ya kamata ayi gwajin jini saboda yiwuwar ya kwashi wata lalurar ta hanyar masha'ar da ya aikata a baya .
Allah ne mafi sani

Amsawa

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
28/10/2017

Share this


0 comments:

Post a Comment