Siffofin Aboki Nagari !!! Dr Jamilu Yusuf Zarewa

*Tambaya:*

Assslamu alaikum Malam ina da abokai da yawa, amma ina so ka ba ni shawara?

*Amsa:*

Wa alaikum assalam, To dan'uwa Aboki yana da mutukar mahimmanci a rayuwar mutum, idan ya zama abokinka mutum ne mai himma, sai kai ma ka samu himma kamar yadda ake cewa zama da madaukin kanwa yana kawo farin kai, haka nan idan ya zama mutumin banza sai ya yi maka tasiri, Abu Musa Al’ash’ari ya rawaito hadisi daga Annabi ((s.aw.)) yana cewa (misalin aboki na gari da abokin banza, kamar misalin mai daukar turare ne da mai hura zuga-zugi, mai daukar turare ko dai ya shafa maka ko ka sayi turare a wurinsa ko kuma ka ji kamshi mai dadi a wurinsa, mai hura zuga- zugi kuma ko ya kona maka kaya ko ka ji wari a wurinsa) Bukhari ne ya rawaito
Kuma wani malami yana cewa:
• idan ka kasance a cikin mutane, to ka yi abota da zababbensu, kada ka yi abota da halakakke saiku halaka tare.
• Idan kana so ka san waye mutum, to ka tambayi abokinsa, saboda kowanne aboki da abokinsa yake koyi .
Wani kuma yana cewa:
• Kar ka aboci malalaci a kowanne hali, da yawa mutumin kirki yana lalacewa ne idan ya hadu da mara kirki.
• Dakiki yana saurin tasiri akan mai kokari, ba ka ganin garwashe idan aka saka shi a toka shi ma sai ya zama toka.
Da fatan za ka kula da abin da ya gabata.
Allah na mafi sani

*Amsawa*✍🏻

*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*
11/11/2017

Share this


0 comments:

Post a Comment