Wanda Ya Tuba Daga Zina Saboda HIV, Allah Zai Amshi Tubansa !!!Dr Jamilu Yusuf Zarewa


Tambaya

Assalamu Alaikum malan, mutumen da yake mazinacine an masa wa'azi amma yaki ya daina...... Har sai da aka tabbatarta masa da cewa cutar HIV ta kama shi sannan ya tuba... To Allah gafarta malan miye matsayin wannan tubar tasa?

Amsa

Wa alaikum assalam, In har ya tuba tuba ingantacce, Allah zai iya amsar tubansa.

Annabi S.a.w. yana cewa: "Allah yana amsar tuban bawa mutukar bai zo gargarar mutuwa ba", kamar yadda Tirmizi ya rawaito kuma ya kyautata a hadisi mai lamba ta: (3537), a wani hadisin kuma yana cewa "Duk wanda ya tuba kafin rana ta fito daga yamma Allah zai amshi tubansa", kamar yadda Bukhari ya rawaito a sahihinsa a lamba ta: (6141).

Hadisan da suka gabata suna nuna cewa ana karbar tuban bawa ko da kuwa ya shiga rashin lafiyar da zai iya mutuwa a cikinta.
Kasancewar ya samu cutar HIV ya daina ba zai hana a amshi tubansa ba, tun da akwai wadanda suna da cutar amma suna yi, tun da cutar ba ta hana jindadin zinar kwata-kwata.

Wanda ya bar zunubi saboda gajiyawa za'a rubuta masa alhakinsa cikakke, kamar yadda hadisi mai lamba (6672) a Bukhari  ya yi nuni zuwa hakan.
Allah ne mafi sani

Amsawa

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
29/10/2017

Share this


0 comments:

Post a Comment