Fatawar Rabon Gado (152) Dr Jamilu Yusuf Zarewa


*Tambaya*

Assalamu Alaikum Dr, Allah ya kara fahimta dan Allah rabon gado ne malam: 'ya'yan mutun daya ne su uku sai biyu suka mutu suka bar daya, shi wanda yake raye be taba haihuwa ba sukuma wa'yanda suka rasu suna da 'ya'ya, ya rabon zai zama .A yayan akwai maza akwai mata mata, maza hudu mata shidda Allah yasa mudace.

*Amsa*
Wa alaikum assalam, Za'a raba gadon ne ga 'ya'yansu kawai.

 Yana daga cikin ka'idojin rabon gado wadanda malamai suka cimma daidaito akansu: "Dukkan 'yan'uwa ba sa gado mutukar a cikin 'ya'yan mamaci akwai namiji".

Allah ne mafi sani.

*Dr, Jamilu Zarewa*

13/11/2017

Share this


0 comments:

Post a Comment