Na Zama Shugaban Karamar hukuma, Menene Mafit !!! Dr Jamilu Yusuf Zarewa

Tambaya

Assalamu alaikum. Malam an sanya ni shugaban karamar hukumarmu, ina neman shawarar yadda zan gudanar da mulki ???


Amsa
Wa alaikum assalam

To dan'uwa ga wata wasiyya mai muhimmanci, in har ka rike ta za ta zamar maka jagora::

Lokacin da Umar bn abdul'aziz Allah ya yi masa rahama ya zama halifan musulmai, sai ya kira Salim bn Abdullah da Muhammad bn Ka'ab da Raja'a bn Haiwah sai ya ce musu:
" Hakika an jarrabe ni da wannan bala'i ku ba ni shawara" !!!!

Sai Salim bn Abdullah Allah ya yi masa rahama ya ce masa :  "Idan kana son ka tsira to ka azumci duniya, kar ka yi buda-baki, sai lokacin da ka mutu" 

Shi kuma Muhammad bn Ka'ab Allah ya yi masa rahama cewa ya yi da shi : "Idan kana son ka tsira daga azabar Allah to babba daga cikin musulmai ya zama babanka, matsakaicinsu kuma ya zama dan'uwanka, karaminsu kuma ya zama kamar Da a wajanka, don haka sai ka girmama babanka, ka karrama dan'uwanka, ka ji tausayin danka".

Bayan sun gama fadin nasiharsu sai Raja'a bn Haiwa Allah ya yi masa rahama ya ce masa : "Idan kana son ka tsira daga azabar Allah, to ka sowa musulmai abin da kake sowa kanka, ka ki musu abin da kake kiwa kanka, sannan in ka mutu shikenan, saidai ina ji maka tsananin tsoro ranar da duga-dugai suke zamewa"
SIYARI A'ALAMIN NUBALA'A 15\448.

In har ka rike wannan Allah zai iya ba ka nasara !!!
Allah ne mafi sani

Amsawa

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

21/12/2017

Share this


0 comments:

Post a Comment