Shakka Ba Ta Gusar Da Abin Da Yake Tabbas!!! Dr jamilu Yusuf Zarewa


Tambaya

AsSalamu alaikum
Malam Dan Allah mafita nake nema nakasance cikin matsanancin kokonto, a sallah da alwala, na dade inayi nayi shekaru km ina addua Allah ya yayemin SBD na damu matuka to yanxu abin yana Neman yayi yawa idn nayi sallah sai inta kokonto bayan km nasan tabbas nayi, amma xuciya sai ta rinjaya akan insake sai inyi raka'a da dama a sallah, to hakama idn nayi alwala sai inji kmr ta karye. Malam Dan Allah a taimakamin yadda xanyi indaina abin yana damuna matuka musamman ynx da yake kara yawa. Km nadage wajen yin azkhar, ataimaka min malam.

*Amsa*
Wa alaikum assalam, Ki yawaita Istigfari, saboda yawan zunubai ya jawo matsaloli.

Ki dinga amfani da abin da ya rinjaya a zuciyarki, kar ki rinka waigawa zuwa waswasin Shaidan, mutukar ba ki samu abin da ya goge yakininki ba.

Ibnu Uthaimin a cikin littafinsa Manzumatul Kawa'idul Fiqhiyya wal-usuliyya ya fadi wurare uku da ba'a waigawa zuwa kokwanto, daga ciki akwai: Idan kokwanto ya yawaita.

Yana daga cikin ka'idojin sharia wadanda malamai suka cimma daidaito akansu: "Shakka ba ta gusar da abin da yake tabbas.

Tun da kina da tabbaci akan aikinki, me yasa za ki waiga zuwa ga kokwanto ?

Yawan sake ibada saboda kokwanto yana jawowa mutum ya tsani ibadar, tare da cewa Allah bai wajabta masa hakan ba.

Allah ne mafi sani

*Dr. Jamilu Yusuf Zarewa*

16/11/2017

Share this


0 comments:

Post a Comment