FATAWAR RABON GADO (157) Dr Jamilu Yusuf ZarewaTambaya

Assalamun'alaikum malam Dan Allah ina tanbayane akan rabon gado mace ta rasu tabar yara biyar uku maza biyu mata da mahaifiyanta Amma bata da miji kuma tabar kudi Naira dubu dari uku da Hamsin (350,000) idan za'a raba kudin Dan Allah Yaya za'ayi ???

Amsa

Wa alaikum assalam, Za'a bawa mahaifiyarta naira (58,333) sai kuma a bawa kowacce mace (36,458) sai kuma a bawa kowanne namiji (72,916).
Akwai naira biyu zuwa uku da za su ragu, da fatan za su yiwa juna afuwa ko kuma su bawa wanda ya raba musu gadon.

Allah ne mafi sani

Amsawa

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
17/01/2018

Share this


0 comments:

Post a Comment