MIJINA BA YA SON HAIHUWA, KO YANA HALATTA NA HANA SHI KAINA ??? Dr Jamilu Yusuf Zarewa


Tambaya

Assalamu alaikum.  Malam ina da matsala  tsakanina da mijina, baya son haihuwa ko saduwa muka yi  saidai  ya zubar  a waje,  Ga shi  kuma  yarinyar mu  daya, ita  ma  bai damu  da  ita  ba,  ina  da laifi  In na  hana  shi  kaina  ??

Amsa

Wa alaikum assalam To 'yar'uwa  yana  da kyau  ki Sani cewa ya Halatta a samu tazara  a tsakanin  iyali, abin da musulunci  ya hana  shi ne kin haihuwa  kwata-kwata,  saboda  babbar  manufar  aure  shi ne hayayyafa, don a samu  wadanda za su bautawa  Allah.

 Zubar da maniyyi a wajan  Farji  ya halatta saboda hadisin Jabir wanda yake cewa "Mun kasance muna yin azalo (zubar da maniyyi a waje yayin saduwa) a lokacin da Qur'ani yake sauka, kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 4911.

Hadisin da ya gabata  yana  nuna  cewa: Bai halatta  mace  ta hana  mijinta  kanta ba saboda  hujjar  yana  AZALO, tun da Alqur'ani  bai haramta  ba.

Saduwa rukuni ne  babba a aure, Wannan yasa Annabi  S.A.W. ya ce: (Mace ta amsa kiran  mijinta  ko  da tana  kan  kaskon  tuya  ya  kira ta,  sannan la'ana  ta  tabbata  ga  wacce  mijinta ya  yi  fushi  da  ita,  saboda  ya  neme  ta ba ta ba  shi  hadin-kai ba.

Kula  da  abin  da mutum  ya  haifa  wajibi  ne,  ciyar  da  su  kuma  sadaka ne, Wannan yasa  za  ki dinga  yiwa  mijinki  nasiha  cikin  ladabi don ya  fahimci  gaskiya .

Allah ne mafi sa ni

Amsawa

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
21/01/2018

Share this


0 comments:

Post a Comment