Fatawar Rabon Gado (160) Dr Jamilu Yusuf ZarewaTambaya

Assalamu alaykum malam, mahaifiyar mu ta rasu ta haifemu mu 10 maza 7 mata 3 bata da mahaifi da mahaifiya amma tana da yan uwa da suke ciki daya maza da mata su bakwai. Shin suma ya' uwan nata sunada gadon ta?

Amsa

Wa alaikum assalam, Za'a raba muku dukiyar ne duka, duk namiji ya dau rabon mata biyu .

Dukkan 'yan'uwa ba sa gado, mutukar mamaci yana da Da namiji, ko da kuwa guda daya ne.

Allah ne mafi sani

Amsawa

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
19/01/2018

Share this


0 comments:

Post a Comment