Ina Na San Nafilolin Rawatib? Dr Jamilu Yusuf Zarewa*Tambaya*

Salaamoon alaykoom, malam Dan Allaah ina son ingancin wadannan sallolin nafilan 1- raka'ah 12 a wuni Allaah zai gina wa mutum gida a aljannah 2- raka'a takwas kafin sallan azahar da bayan sa wuta ba zai ci shi ba 3- raka'ah hudu kafin sallan la'asar

*Amsa*
Wa alaikum assalam, tabbas hadisi ya tabbata cewa: (Duk wanda ya yi sallolin nafila raka'ioi 12 Allah zai gina masa gida a cikin aljanna.

Zaid bin Arkam daya daga cikin sahabban Annabi (SAW) ya fassara wadanann nafiloli da Sifa kamar haka:
Raka'a biyu kafin sallar asuba, raka'a hudu kafin sallar Azahar, raka'a biyu bayanta, raka'a biyu bayan sallar Magriba, sai kuma raka'a biyu bayan sallar Isha.

Ragowar abin da ka fada ban san shi ba a hadisai a ingantattu, rashin sanina kuma baya nuna babu shi.

Allah ne mafi sani

*Dr Jamilu Zarewa*

13/02/2018

Share this


0 comments:

Post a Comment