Ta ki Yarda Da Mijinta Saboda Tana Azumin Nafila ??? Dr Jamilu Yusuf Zarewa


Tambaya

AssalamuAlaikum.
Mallam inna da tambaya ? Yaya hukuncin Matar da miji ya bukacheta sannan tana Azumin sunna. Ta ki ta Aminche mishi


Amsa
Wa aleikum assalam,

ta yi kuskure ya kamata ta amsa kiran mijinta, saboda azumin sunna  ya halatta a karya shi ko da babu dalili, Annabi (SAW) yana cewa"Mai azumin nafila sarkin kansa ne ina ya Ga dama  ya cigaba da azumin, in kuma ya so ya  karya " kamar yadda Tirmizi ya rawaito a Sunan

Allah  ne mafi sani.

Dr, Jamilu Zarewa

30/1/2018

Share this


0 comments:

Post a Comment