Mijina Ya Sake Ni Ina Shayarwa, Ko Zan Iya Idda Da Wata Ukku?? ? Dr Jamilu Yusuf Zarewa


*TAMBAYA*

Assalamu alaikum warahmatullah.
Malam ga tambayata kamar haka watace akasaketa tana shayarwa kuma batayin al'ada toshin xata iya yin aure bayan wata uku ko kuma sai tajira ta yaye yaronta har taga al'adanta Kafin tayi auren nagode

*AMSA*

Wa alaikum assalam, za ta jira jini uku, ko da kuwa sai ta yi shekara uku, kafin ta kammala iddar, saboda Allah ya rataye iddar matar da aka saka, kuma ba ta yanke kauna daga haila ba da jini uku, kamar yadda aya ta : 228 a suratul Bakara ta tabbatar da hakan.

 Allah ne mafi sani

*Amsawa*✍🏻

*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*
18/02/2018

Share this


0 comments:

Post a Comment