ZAN IYA CIGABA DA ZAMAN AURE DA MASHAYIN GIYA?? Dr Jamilu Yusuf Zarewa


Tambaya

Assalamu alaikum malam tambayata mijinane  mutum Mari Shaye Shaye kuma Allah  ya azurtamu da haihuwa Yara  hudu  Don Allah  meye hukunci zamana dashi a addini shin babu laifi ko kuma akwai laifi

Amsa:
Wa alaikum assalam, Ki yi kokari wajan yi masa nasiha Allah zai iya shiryar da shi.

In har kina son shi za ki iya cigaba da zama da  shi.

Wanda yake shan giya fasiki ne, saboda yana aikata babban zunubi, saidai a musulunce tun da zunubin da yake aikatawa bai kai  kafurci ba ya halatta ki cigaba da zaman aure da shi mutukar kina kaunar shi.

Allah madaukakin sarki ya shar'anta saki saboda tunkude cutarwa daga ma'aurata, mutukar ba za ki iya tsayawa da hakkokinsa ba,  ya halatta ku rabu, tare da cewa duba makomar yaranku yana da muhimmanci.
Allah ne mafi sani

Dr Jamilu Zarewa
24/3/2018

Share this


0 comments:

Post a Comment