Zan Iya Zamiyar Bashina Daga Zakka?? Dr Jamilu Yusuf Zarewa


Tambaya

Assalamu Alaikum. ya sheikh. Ina da tambaya. Idan ina bin mutum bashin kudi kuma zanyi zakka, zan iya cewa na bar mai abinda nake binshi a matsayin zakka?

Amsa
Wa alaikum assalam

Malamai sun yi sabani a wannan mas'alar zuwa zantuka guda biyu:

1. Ba ya halatta mutum ya mayar da bashin da yake bin wani a matsayin zakka,  saboda Zakka hakkin Allah ne,  yin hakan kuma zai zama ya amfanar da kansa da zakkar saboda in ba ta hanyar ta ba da kudinsa ba za su fito ba, Wannan ita ce fatawar  Malaman Hanafiyya da Hanabila sannan kuma ita ce fatawar malaman Malikiyya in ban da Ash'habu, hakan kuma shi ne mafi inganci a wajan Shafi'iyya.

2. Ya halatta ya mayar da  bashinsa da yake kan wani ya zama Zakka, saboda in da zai ba shi zakkar ya dauke ta ya biya shi bashi da ita da ya halatta ya amsa, wannan ita ce fatawar Ash'habu daga Malikiyya sannan kuma Kauli ne a mazhabar Shafi'iyya kamar yadda Nawawy ya ambata a Almajmu'u.

Don neman Karin bayani duba: Almausua Alfiqhiyya 23/131.

Duk da cewa babu nassi yankakke bayyananne  a mas'alar a iya bincikenmu, Saidai fatawar mafi yawan malamai na rashin yin ZAMIYAR ita ce ta fi rinjaye, saboda kubutar da wuyaye daga yiwuwar kuskure yana da kyau sannan fita daga sabanin Malamai abin so ne.

Allah ne mafi sani

Dr, Jamilu Zarewa

19/04/2018

Share this


0 comments:

Post a Comment