FATAWAR RABON GADO (172) Dr Jamilu Yusuf Zarewa


*Tambaya*

Assalamu alaikum Mutum ne ya rasu
Ya bar matansa biyu, da 'yarsa guda daya...
Sai 'yan uwansa mata guda hudu da namiji guda daya, Wadanda suke tsatso daya
Tambaya, su 'yan uwan nasa suma zasu gajeshi..

*Amsa*

Wa alaikum assalam Za'a raba gida(8) matansa kashi (1) 'yarsa kashi (4) Ragowar a bawa 'yan'uwansa su raba, DUK namiji ya dau rabon mata biyu.

Allah ne mafi sani

*Amsawa*✍🏻

*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*
25/04/2018

Share this


0 comments:

Post a Comment