HUKUNCIN CEWA MALAMI (RADIYALLAHU ANHU )- Dr Jamilu Yusuf Zarewa*Tambaya*

Assalamu alaikum malam Shin ya halasta ace ma wani babban sheikh ko malamin da ake ganin rikonsa da addini sosai (radiyallahu anhu ? ) bayan rasuwarsa ?

*AMSA :*

Wa alaikumus salam Mafiya yawan malamai sun tafi akan hallacin haka , kamar yadda Nawawy ya fada a Majmu'u, sharhin Muhazzab, saidai abin da ya fi shahara shi ne sahabbai kawai ake fadawa wannan jumlar, wanda kuma ba sahabi ba, ana ce masa (RAHIMAHULLAHU), in kuma yana raye (HAFIZAHULLAHU)

Allah ne mafi sani

*Amsawa*✍🏻

*DR. JAMILU YUSUF  ZAREWA*
3/6/2014

Share this


0 comments:

Post a Comment