MIJINA YA SAKE NI DA DANYAN GOYO, YAYA IDDATA ? Dr Jamilu Yusuf Zarewa

*_Tambaya_*

Assalamu Alaikum, Dr. Tambayace- mace mijinta ya sake bayan ta haihu da danyen goyo. Ya iddarta zata kasance? Allah ya karawa Dr. Ikhlasi.

*_Amsa_*

Wa alaikum assalam.
Za ta jira jini uku Kamar yadda aya ta (228) a Suratul Bakara ta tabbatar da hakan, ba za ta yi aure ba har sai ta kammala su

Allah ya kara mana iklasi a duka lamuranmu.

Allah ne mafi sani.

*_Dr. Jamilu Zarewa_*

25/06/2018

Share this


0 comments:

Post a Comment